Épisodes

  • Abun Da Masu Ruwa Da Tsaki Ke Yi Na Dakile Laifuka A Wurin Matasa
    Dec 4 2025

    Send us a text

    Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa.
    In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka su a cell?


    ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma da satar mutane don kudin fansa a tsakanin matasa.

    Ko yaya wannan dabara take aiki?


    Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari a kai.

    Voir plus Voir moins
    25 min
  • Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Shi
    Dec 2 2025

    Send us a text

    Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.


    An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da wannan cuta. Abin damuwa shi ne cewa yawancin lokuta ana gano cutar ne a kurarren lokaci, wanda hakan ke sa magani ya yi wahala kuma ya rage yiwuwar ceto rayuwar wanda ya kamu da shi.


    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    Voir plus Voir moins
    29 min
  • Halayen Da Ambasadoji Ya Kamata Su Mallaka Kafin Tura Su Wasu Kasashe
    Dec 1 2025

    Send us a text

    A mafi yawan ƙasashen duniya, ana ɗaukar jakadu a matsayin fuskar ƙasa kuma ginshiƙan hulɗar diflomasiyya. Saboda haka, akwai muhimman halaye da suke tilas jakadan ƙwarai ya mallaka domin ya wakilci ƙasarsa cikin mutunci, da nagarta da kwarewa.


    Tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sunayen jakadu da yake sa ran majalisar kasa ta tantance ne dai batun ke ta shan suka daga manazarta kan sunayen da ya fitar.


    Ko wadanne irin halaye ya kamata jakada ya mallaka a yayin da za a tura shi a matsayin wakili a wata kasa?


    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    Voir plus Voir moins
    24 min
  • Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini
    Nov 28 2025

    Send us a text

    Sheikh Dahiru Usman Bauchi, fitaccen malamin addinin Musulunci, masanin tafsiri, kuma jagoran darikar Tijjaniyya, shahararre ne saboda iliminsa mai zurfi da tasirin da ya yi a fagen addini da tarbiyya a Najeriya da ma ƙasashen Yammacin Afirka.

    Sheikh Dahiru Bauci ya shafe sama da shekaru saba’in yana koyar da ilimi, ya gudanar da tarukan tafsiri a duk shekara, ya gina makarantu, ya kafa cibiyoyi, kuma ya ba da ilimi ga dubban almajirai hanyoyin da suka taimaka wajen yaɗa ilimin addini cikin lumana da biyayya ga Allah Madaukakin Sarki. Rayuwarsa ta kasance tsantsa ta tsoron Allah, tawali’u, da ayyukan alheri.

    A wannan waiwayen, za mu duba manyan abubuwa da suka yi fice a cikin rayuwar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauci da irin tasirin sa ga al’umma, da darussan tafsirin Alƙur’ani da ya yi wa duniya, da irin irin kyawawan dabi’u da ya bari a matsayin abun gado ga musulmi.

    Voir plus Voir moins
    24 min
  • Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
    Nov 27 2025

    Send us a text

    A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi dacewa gwamatani ta yi amfani da shi wajen kawo karshen wadannan matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa tsawon shekaru.


    Yayin da wasu ke ganin amfani da karfin soji ne kadai hanyar da zai kawo karshen wannan matsala, wasu na ganin tattaunawa ne kadai mafita, wasu har ila yau na ganin idan aka yi amfani da gaurayen biyun zai fi dacewa.


    Ko wanne daga cikin wadannan hanyoyi ne idan gwamnati ta yi amfai dashi ko da su don magance wannan matsala?

    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    Voir plus Voir moins
    22 min
  • Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta
    Nov 25 2025

    Send us a text

    Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita.


    Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita.
    Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan.
    A Najeriya kadai, ana kiyasta cewa fiye da yara 150,000 ake haifa da cutar Sikila a kowace shekara — hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan masu fama da cutar Sikila a duniya.


    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan cutar amosanin jini don gano yadda masu fama da ita ke ji a rayuwar su.

    Voir plus Voir moins
    24 min
  • Halin Da Shirin Samar Da Tsaro A Makarantun Najeriya Ke Ciki
    Nov 24 2025

    Send us a text

    A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative.


    Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa makaranta cikin tsaro ba tare da fargabar hare-hare daga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga ba.


    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne akan wannan shiri da kuma halin da yake ciki a wannan lokaci.

    Voir plus Voir moins
    24 min
  • Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu
    Nov 21 2025

    Send us a text

    Hukuncin da kotun tarayya ta Abuja ta yanke wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya sake tayar da kura a tsakanin magoya bayansa, ‘yan yankin Kudu maso Gabas, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya.


    Yayin da gwamnati ke cewa hukuncin ya biyo bayan dogon shari’a da hujjoji da suka tabbatar da aikata laifukan da ake tuhumarsa da su, wasu na ganin batun na da matuƙar sarkakiya musamman ma yadda iyalansa da magoya bayansa ke kallon wannan hukunci.


    Shin ko yaya ‘yan uwan Nnamdi Kanu suka kalli wannan hukunci?

    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    Voir plus Voir moins
    25 min